Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Rage Farashin Takin Zamani Da Kuma Bada Tallafin Kayan Noma


Injunan Casar Shinkafa
Injunan Casar Shinkafa

Gwamnati ta fara cika alkawarinta ga manoma su kuma sun fara darawa

Kasashen Sin Da Ingila sun shiga kawancen huldar kasuwanci na sayan ridi, rogo da waken suya daga hanun kananan manoma na jihar Taraba ta hanyar rabon ingantaccen iri kyauta don baiwa manoman kwarin gwiwa.

Gwamnan jihar Taraba Arch, Darius Dickson, ne ya furta haka a lokacin da yake kaddamar da saida takin zamani ton talatin na NPK da Yuriya ga manoma albarkacin daminar bana akan Naira dubu hudu da dari biyar kowani buhu abinda ke nuna rangwamen kashi hamsin idan aka kwatanta da farashinsa a hanun ‘yan kasuwa.

Da yake kaddamar da sayar da takin zamani, ya kuma bada injunan casar shinkafa rance ga manoma da kuma rabon ingantattun irin rogo, ridi da waken soya kyauta.

Wannan na daga cikin matakan da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke dauka na farfado da sana’ar noma don rage dogaron tattalin arziki kan man fetur inji gwamna Arch, Darius Dickson Ishaku na jihar Taraba.

Akwai matakan ladabtarwa ga mutanen da za su nemi karkatar da takin da ma saura kayayyakin noma da gwamnati ta tanada inji gwamnan, kana ya baiwa manoma tabbacin samar masu da kasuwannin a gida da ketare da zasu sayarda anfanin gonarsu bayan girbi don kauda da fargabar wuraren adana anfanin gona da inda zasu saida su.

Da yake bayanin yadda kananan manoma a jihar Taraba suka karbi shirin saida takin, rabon ingantattun irin shuka da ma injunan casar shikafa, shugaban kungiyar manoma ta kasa reshen jihar Taraba Mal, Abdulrahaman Miyam ya ce a karon farko za a saida taki Naira dubu hudu da dari biyar a jihar, ya nuni da tallafi na injunan ban ruwa dari biyar ga manoma inda dari uku da arba’in da biyar da suka anfana da tallafin a arewaci da kudancin jihar suka ce tallafin ya taimaka masu wajen habaka sana’ar noman rani.

Mal. Miyam ya ce kananan manoman jihar sun anfana daga shirin rance da shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar bara na Ancho Borrowers ga manoman shikafa na rani.

Allah ya albarkaci jihar Taraba da kasar da ya dace da noma kowani irin anfanin gona da kiwon dabbobi a arewa maso gabashin Najeriya dake da damina mai tsawon watanni tara.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:06 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG