Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An rantsar da shugaban 'yan adawa a matsayin sabon Shugaban Zambia


Sabon Shugaban Zambia Micheal Sata kafin a rantsar da shi
Sabon Shugaban Zambia Micheal Sata kafin a rantsar da shi

An rantsar da dadadden shugaban ‘yan adawan Zambia Michael

An rantsar da dadadden shugaban ‘yan adawan Zambia Michael Sata, a matsayin shugaban Zambiya a yau Jumma’a, wanda hakan ya zama karo na biyu da kasar ta canza gwamnati a demokaradiyyance, tun bayan samun ‘yancin kanta daga Burtaniya.

Hukumar Zaben Zambia ta bayar da sanarwa da safiyar yau Jumma’a cewa karbabben shugaban dan shekara 74 ya doke shugaba mai ci Rupiah bayan sun yi kare-jini biri jinni a zaben shugaban kasar da ya gamu da ‘yan tashe-tashen hankula nan da can a fadin kasar.

A wani taron manema labarai, Shugaba Banda, mai cike da kwalla, ya amince da shan kayen, yana mai cewa “mutanen Zambia sun ce wani abu, kuma wajibi ne dukkanninmu mu saurare su.” Mr. Banda ya kuma gargadi magoya bayansa cewa akul su yi ramuwar gayya, kara da cewa “yanzu ba lokacin tashin hankali ba ne.”

Magoya bayan Sata sun bazu bisa tituna suna ta murna bayan da hukumar zaben ta bayar da sanarwar, nan da nan bayan karfe 12 na daren kasar.

Bayan zaben na ran Talata, an sami rahotannin tashe-tashen hankula, saboda bacin ran da ya biyo bayan jinkirin da hukumar zaben ke nunawa wajen sanar da sakamakon zaben. ‘Yan adawa da dama sun yi fargabar cewa, jinkirin zai taimaka wa hukumar zaben ta karkatar da sakamakon don amfanar Mr. Banda.

Kafin fara zaben, Mr. Sata, wanda ake wa lakabi da “Babban Kububuwa” saboda irin lafazinsa da magana gaba gadi, ya zargi hukumar zaben da shirin yin magudi ta wajen amfani da kuri’un da aka riga aka dangwala, zargin da ita kuma hukumar ta yi watsi da shi.

XS
SM
MD
LG