Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sallami Daya Daga Cikin masu Bin Kadin Shari'ar Umar Faruk Abdulmutallab


Zanen bayyanar Umar faruk Abdulmutallab (Hagu) a cikin kotu a birnin Detroit.
Zanen bayyanar Umar faruk Abdulmutallab (Hagu) a cikin kotu a birnin Detroit.

Mai shari'a ta ce akwai wata matsala dangane da wata mace 'yar asalin Najeriya da aka zaba cikin gungun masu bin kadin shari'ar amma ba ta yi bayani ba.

Wata mai shari’a a nan Amurka ta sallami daya daga cikin gungun mutane masu bin kadin shari’ar wani dan Najeriya da ake tuhuma da kokarin tarwatsa wani jirgin saman fasinja na Amurka da bam da ya boye cikin kamfansa a 2009.

Yau alhamis mai shari’a Nancy Edmunds ta sallami wata ‘yar asalin Najeriya daga cikin masu bin kadin shari’a da aka zaba, ‘yan mintoci kadan a bayan da lauyoyi masu gabatar da kara da masu kare wanda ake tuhuma suka yarda da zaben masu bin kadin shari’a 12 da wasu guda 4 na wucin gadi.

Mai shari’a Edmunds ta ce akwai wata matsala game da ita wannan mai bin kadin shari’ar amma ba ta yi bayanin matsalar ba. Lauyoyi masu gabatar da kara da masu kariya sun shafe kwanaki biyu su na tambayoyi wa mutane fiye da 40 domin zabo wadanda zasu bi kadin shari’ar Umar Faruk Abdulmutallab.

A yau alhamis suka cimma daidaituwa kan masu bin kadin su 12 da kuma guda 4 masu zaman wucin gadi, kuma babu dayansu da ya nuna adawa da shigar da ita wannan ‘yar Najeriya tun fari a cikin masu bin kadin shari’ar.

Dokokin kotun sun tanadi cewa za a maye gurbinta da daya daga cikin mutane 4 masu bin kadi na wucin gadi, sannan sa a sake zaben guda na wucin gadi daga waje.

A ranar talata za a fara gabatar da jawaban bude shari’ar.

Abdulmutallab yana fuskantar tuhume-tuhume da dama ciki har da hada baki don aikata ta’addanci dangane da wannan lamari da ya faru a cikin wani jirgin saman da ya taso daga Amsterdam zuwa Detroit a ranar 25 ga watan Disambar 2009. Fasinjoji sun danne saurayin dan Najeriya a bayanda nakiyar da ya boye ta kasa tashi.

Abdulmutallab dai ya nada kansa a zaman lauyan kansa a lokacin shari’ar, amma wani lauyan wucin gadi da kotun ta nada masa shi ne yayi akasarin tambayoyi a lokacin da ake tace masu bin kadin shari’ar. Shi wannan lauya mai suna Anthony Chambers ya rubuta ma kotun wasika jiya laraba yana kukar cewa akasarin masu neman shiga gungun bin kadin wannan shari’ar sun bayyana cewa su na fusace da jin zafi tare da neman daukar fansa a kan shi Umar Faruk Abdulmutallab.

XS
SM
MD
LG