Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tayar Da Maganar Zargin Rashawa Ga Jami'an Sojan Ruwan Amurka


Ma’aikatar shari’ar Amurka ta sake tada maganar nan da ake zargin wasu tsoffin jamia’an sojan ruwa su 8 da kuma wasu da suka bar aiki daga cikin su akan zargin cin hanci da rashawa, wanda dan kwangilar nan mai suna Fat Leonard ke kan gaba.

Wannan batun dai yasa Amurka hasarar a kalla dala miliyan 36, kuma yau shekaru 4 kenan ake kan binciken wannan batu, abin da mahukuntan na Amurka suka ce mutane kusan 200 ke cikin wannan badakalar.

Wannan bakaramin cin amanar kasa bane kuma da kuma tozarta aikin sojan ruwa, wanda manya-manyan jami’an soja ruwa suka aikata, inji babban mukaddashin mai shara’a Alana Robinson a jiya talata.

Ma’aikatar shari’ar tace Rear Admiral Bruce Loveless, daya daga cikin manyan sojojin ruwa mai kula da sashen tattara bayanan sirri dake ma’aikatar tsaron Amurka na Pentagon na cikin wadanda ake tuhuma a wannan abin fassalar, sai kuma wasu jamia’an sojan ruwa su 3 da suka yi murabus, haka kuma akwai warrant officer da kuma kwamanda guda.

Ana tuhumar wadannan jamia’an sojan ruwan da karban cin hanci da rashawa, kawo wa aikin shari’a cikas, tare da kantara karya gamasu bincike na gwamnatin tarayya.

Tuhumar da ake wa wadannan mutanen shine karban na goro daga dan kwangilar nan dake zaune a kasar Singaphore Leonard Francis wanda tuni ya amsa laifin sa, cewa ba shakka sun cuci ma’aikatar sojan ruwa miliyoyin daloli, shi dai wannan dan talikin ana masa lakabi da FAT LEONARD.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG