Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tsaida Ranar Zaben Shugaban Kasar Burkina Faso


Shugaban rikon kwarya a Burkina, Michel Kafando,
Shugaban rikon kwarya a Burkina, Michel Kafando,

An cimma matsayar cewa zaben shugaban kasar nan na Burkina Faso da yunkurin juyin mulkin da aka so yi ya hana a gudanar da shi, yanzu za’a gudanar da shi ran 29 ga watan Nuwambar wannan shekara

Shi wannan zaben da aka so a hada shi da na ‘yan-majalisar dokokin kasar, wanda kuma a da aka shirya za’ayi ran 11 ga watan nan na Oktoba, ana yi mishi kallon kamar wani sabon mataki ne wannan kasar dake Afrika ta Yamma ta dauka don inganta akidar demokradiya amma kuma sai yunkurin juyin mulkin da soja masu biyayya ga hambararren shugaban kasar Blaise Campaore suka so yi, yasa ala tilas aka dage yinsa.

A ran 17 ga watan Satumba ne wannan tarzomar juyin mulkin ta jefa Burkina Faso a cikin rikicin kwannaki shidda kafin yunkurin

A cikin hirarsu da Mahmud Lalo, Dr Ja'afar Dabai na jami'ar Kampala ta kasar Uganda ya bayyana cewa, akwai alamun zaben zai yiwu kuma zai yi armashi, kasancewa kasar da kuma gwamnatin rikon kwarya tana da goyon bayan kasashen yammacin Afrika da kum sauran kasashen duniya.

Yace galibin 'yan kasar Burkina Faso da bayan gwamnatin da ta shuge suna goyon bayan bincike masababin mutuwar marigayi Thomas Sankara.

Ga Hirar Mahmud da Dr Ja'afar

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG