Accessibility links

An Yanke Ma Faizal Shahzad Hukumcin Daurin Rai Da Rai


An Yanke Ma Faizal Shahzad Hukumcin Daurin Rai Da Rai

An Yanke Ma Faizal Shahzad Hukumcin Daurin Rai Da Rai

A watan Yuni Shahzad, Ba-Amurke haifaffen kasar Pakistan ya amsa laifin kokarin tayar da bam a dandalin Times Square na New York

An yanke hukumcin daurin rai da rai a kan wani Ba-Amurke haifaffen kasar Pakistan wanda yayi yunkurin dasa bam a dandalin Times Square na birnin New York.

Jiya talata wata mai shari'a ta kotun tarayya a New York ta yanke hukumcin kan Faisal Shahzad mai shekaru 31 da haihuwa.

A watan Yuni Shahzad ya amsa laifuffuka guda 10 da aka tuhume shi da aikatawa na ta'addanci da mallakar makami. A cikin takardun da suka gabatar ma kotu a makon jiya, lauyoyi masu gabatar da kara sun ce Shahzad ya zabi wani wuri a wannan gunduma dake shake da mutane inda yake tsammanin bam din nasa zai fi yin ta'adi.

Masu gabatar da karar suka ce idan da ba a kama Shahzad ba, to yayi niyyar tayar da wani bam din bayan mako biyu a birnin na New York.

Wannan bam da ya dasa dai bai tashi ba, kuma kwanaki biyu bayan yunkurin kai harin na ranar 1 ga watan Mayu, an kama Shahzad a cikin wani jirgin saman dake dab da tashi daga New York zuwa Dubai.

XS
SM
MD
LG