Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Gwajin Maganin Rigakafin da Kamuwa da Ciwon Zuciya A Kasashe Biyar


Kayan gwajin kwayar cutar kanjamau da Amurka ke ba kasashe
Kayan gwajin kwayar cutar kanjamau da Amurka ke ba kasashe

Koriya ta Kudu tana daya daga cikin kasashe biyar da suka yi wani gwajin farko na kokarin rigakafin kamuwa da ciwon zuciya da bugun jini tsakanin wadanda suke fama da cutar kanjamau, da suka fi fuskantar barazanar kamuwa da cututuka.

Ana tara jerin wadanda za a yi gwajin a kansu da aka ba lakabi REPRIEVE, a wani yunkuri da aka bayyana a matsayin sabon salon yaki da kwayar cutar HIV, da nufin taimakawa wadanda ke dauke da cutar su iya rayuwa cikin koshin lafiya.

Za a kashe dala miliyan ishirin kowacce shekara a kan binciken da Amurka ke daukar nauyinsa, wanda ake kyautata zaton za a dauki shekaru shida ana gudanarwa a kan mutane dubu shida da dari biyar.

Za a rika ba mutanen da za a gudanar da binciken kansu dake kasashen Canada, Thailand, Brazil da kuma Afrika ta Kudu karin kwayar magani guda, banda maganin kwantar da kaifin cutar da suke sha kowacce rana. Maganin zai taimaka wajen rage kwayoyin dake cikin jini dake haifar da hawan jini ko bugun zuciya.

Za a sawa mutanen da ake gudanar da binciken a kansu ido sosai cikin shekaru shida masu zuwa domin ganin ko akwai sauyi a lafiyarsu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG