Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Anyi Bikin Cikar Nijar Shekaru 57, Da Ta Samu Zama Jamhuriya


Tambarin Jamhuriyar Nijar
Tambarin Jamhuriyar Nijar

Wannan biki dai yasa an kawata birnin Maradi , amma talakawa mazauna Unguwoyi suna korafi

Anyi bikin cikar jamhuriyar Nijar, shekaru 57, da ta sami zama jamhuriya, a Niamey Babban birnin kasar ta Nijar wanda aka radawa suna Maradi kwalliya.

Bayan tattalin arziki wane irin ci gaba aka samu a cikin harkokin dimokradiya, Malam Abdurahaman Kuli, ya shidawa wakilin muryar Amurka Chaibu Mani , cewa a fuskar siyasa daga shekara 1991, zuwa 1992, sun samu damar kowa ya kirkiro kungiyar siyasar shi, ya kara da cewa bisa fannin ci gaba Nijar yau dunkin mulki ya samu karbuwa ga jama’a.

Wannan biki dai yasa an kawata birnin Maradi a wadansu wurare, amma talakawa mazauna Unguwoyi a cikin lungu sun bayyana cewa fuskar gari ce kadai aka gyara kananan unguyoyi daya kamata a gyara da yi masu kwalbatoci sune suka fi shafar talaka amma ba’a yiba.

A dangin wasani daban daban Maradi ta taka rawar gani a wajen wasanin raya al’adu, sai kuma maganar tda tafi daukar hankalin jama’a itace ta yunkurin juyin milki a kasar ta Nijar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:37 0:00

XS
SM
MD
LG