Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Za'a Iya Komawa Garuruwan da Aka Kwato Ba Yanzu - Maina


Maharba da suke taimakawa wurin yakar Boko Haram a jihar Bono
Maharba da suke taimakawa wurin yakar Boko Haram a jihar Bono

Dan majalisar wakilai da ke wakiltar mazabar Kondiga da Mafa da kuma Dikwa da ke jihar Borno, Muhammad Maina, ya ce lokaci bai yi ba da mutanen yankin za su iya komawa garuruwan da aka kwato daga hannun 'yan Boko Haram.

Dan majalisar ya ce ko shakka babu akwai wasu garuruwan da aka kwato amma idan aka yi la'akkari da yadda garuruwan suke yanzu akwai bukatar jirkintawa.

"Jirkintawar za ta taimaka a samu a sake gina masu muhallansu. Yakamata a tanada masu ruwan sha da harkokin kiwon lafiya da kuma wasu bukatu na yau da kullum." In ji Muhammad Maina.

Banda samarda ruwan sha yace garuruwan suna wari kuma zama cikinsu yanzu zai yi wuya. Ya ce za'a kwashe kusan shekara biyu ana gine-gine da wasu ayyukan kafin mutane su iya komawa. A cewar dan majalisar garuruwan basa zaunuwa yanzu.

Shi ko shugaban karamar hukumar Galaho, Abdulrahaman Abdulkarim ya ce duk da cewa da hadin gwiwar sojojin Chadi an kwato garinsu amma bayan da sojojin suka koma kasarsu 'yan Boko Haram sun sake afkawa garin inda suka hallaka wasu mutanensu..

Alhaji Khalifa Bukar Ram shugaban karamar hukumar Kalebage ya ce har yanzu garinsu na hannun 'yan Boko Haram. Ya ce ya kamata gwamnatin tarayya ta yi wani abu akai.

Ga rahoton Haruna Dauda Biu.

Mutane Ba Zasu Iya Komawa Garuruwan da Aka Kwato daga Boko Haram Ba Yanzu -inji Muhammad Maina - 3'11"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:11 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG