Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ban Ki-moon ya ce Mali ta saki mutanen da ta kama


Shugaban juyin mulkin Mali Amadou Haya Sanogo ke jawabi
Shugaban juyin mulkin Mali Amadou Haya Sanogo ke jawabi

Babban Magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon yayi kiran da a gaggauta sakin mutanen da hukumomin kasar Mali suka kama

Babban Magatakardar MDD Ban Ki-moon yayi kiran da a gaggauta sakin mutanen da hukumomin kasar Mali suka kama suna tsare dasu tun juyin mulkin da soja suka gudanar a watan da ya gabata.

Wata sanarwar dake dauke da sa hannun babban magatakardar na MDD da a fidda aka rarrbawa manema labarai, Mr. Ban Ki-moon ya roki shugabannin sojin da suka yi juyin mulki a Mali da su yiwa Allah su maido da aiki da kundin tsarin mulkin kasar Mali ba tare da sun sauya komai a cikinsa ba domin ci gaba da baiwa tsarin mulkin farar hula muhimmancin da ya kamata. Yace babbar matsalar dake damun kasa da kasa yanzu it ace rashin sanin halin da hambararren shugaban farar hula Amadou Toumani Tour eke ciki, im banda sanin cewa yana gudun mafaka a ofishin jakadancin kasar Senegal dake Bamako, babban birnin kasar Mali.

Talatar da ta gabata ce sojin kasar Mali suka rika bi suna kakkama manyan shugabannin jam’iyyun siyasa akalla su bakwai ana tsare dasu, aka kuma hada wasu jami’an soja masu fada aji da wasu muhimman shugabannin al’umma, kuma ya zuwa yau din nan ana ci gaba da tsaresu. MDD na yin kiran da asako wadannan mutane cikin hanzaari.

XS
SM
MD
LG