Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Birtaniya da Faransa Sun Amince Su Karbi 'Yan Gudun Hijira


'Yan gudun hijira daga Syria
'Yan gudun hijira daga Syria

Faransa da Birtaniya sun amince da karbar dubban ‘yan gudun hijira a jiya Litinin, wadanda yaki ya daidaita a gabas ta tsakiya.

Sai dai yawan da jama’ar da suka yarda za su ba mafakar ya nutse a cikin dimbin masu tururuwar kutsawa cikin Jamus don samun sabuwar rayuwa.

Shugaban Faransa Faransuwa Oland yace kasarsa zata karbi mutane dubu 24 ne ‘yan gudun hijira daga nan zuwa shekaru 2 masu zuwa.

Shima Firayim MinIstan Birtaniya David Cameron ya bayyana za su karbi bakuncin ‘yan gudun hijira guda dubu 20 ne daga sansanin ‘yan Syria da ke Turkiyya, Jordan da Syria.

Sannan ya ce za su samu nutuswa a kasar Birtaniya nan da shekaru 5 masu zuwa, sai dai Mr Cameron yace za su fi maida hankalinsu ga yara kanana da ka iya fadawa cikin hatsarin rayuwa.

Kasashen Turai na fama da matsalar kwararar bakin haure ‘yan gudun hijirar da rabonsu da ganin haka tun lokacin yakin duniya na biyu.

Ga kuma kasar Hungary na ta kokarin datse kan iyakarta da Jamus da ke da karfin tattalin arziki daga kasashen yankin Sakandinebiya.

Duk da haka dubban ‘yan gudun hijirar sun kutsa cikin Jamus din, a inda hukumomi da jamu’sawa suka tarbe su da abinci ‘ya’yansu kuma suka dinga rabawa yaran kayan wasansu.

XS
SM
MD
LG