Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Birtaniya ta kamma shirin bukin cika shekaru 60 da mulkin sarauniya Elizabeth


Shirin bukin mulkin sarauniya Elizabeth
Shirin bukin mulkin sarauniya Elizabeth

Birtaniya zata fara bukukuwan kwanaki hudu na cika shekaru 60 da hawa karagar mulkin sarauniya Elizabeth

Birtaniya zata fara bukin kwana hudu na cika shekaru 60 da hawa karagar mulkin sarauniya Elizabeth, yayinda ake shirin gagarumin buki da wasanni iri iri inda al’ummar kasar suke nuna kishin kasa.

An jera tutucin Birtaniya da ake kira “Union Jack” a kan manyan titunan birnin London inda ake kyautata zaton mutane zasu yi dandazo a jerin gwanon da za a gudanar da kuma sauran bukukuwan na tsawon kwanaki.

Bisa ga dukan alamu, farin jinin Sarauniyar mai shekaru 86 da haihuwa yana karuwa, yayinda mutane da dama dake ji a jikinsu, sakamakon koma bayan tattalin arziki, suke kaulin bukukuwan.

Yarima Charles, dan sarauniyar kuma magajin sarautar, yace bukin wata dama ce ta karamma ta, da kuma nuna yadda kasar da kuma ‘ya’yanta suke kaunarta.

Karon farko, Fadar ta fitar da wadansu hotunan bidiyo da aka dauka a gida, na sarauniya Elizabeth wanda ya nuna rayuwarta.

Sarauniya Elizabeth ta gaji mahaifinta Sarki George bayan rasuwarshi a shekara ta dubu da dari tara da hamsin da biyu, bayan shekara daya kuma, aka nada ta sarauniyar kasashe bakwai masu zumunci da ingila da suka hada da Birtaniya, Canada, Australia, New Zealand, South Africa, Pakistan da kuma Ceylon wadda ake kira Sri Lanka yanzu.

XS
SM
MD
LG