Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bom da Ya Fashe A Iraqi Ya Kashe Mutane 17 da Raunata Wasu 60


Inda ake lugudan wuta a Iraqi
Inda ake lugudan wuta a Iraqi

Mahukunta a kasar Iraqi sun ce fashewar bom a babban birnin kasar Iraqi din wato Bagadaza yayi dalilin mutuwar mutane 17, kana wasu 60 sun samu raunukka daban-daban.

Bom din ko ya tashi ne a cikin wata mota da aka ajiye a wata kasuwar sayar da kayan marmari da na ‘ya’yan itace, akan wani sanannin titin da ake yawan zirga-zirga wanda ke Huriyya, wata unguwa dake arewa maso yammacin birnin, wanda kuma wuri ne da yake da yawan mazaunansa duk ‘yan mashabar Shi’ite ne, wanda hakan yayi dalilin mutuwar mutane 10 kana wasu 30 suka ji rauni.

Haka kuma Jamiaan gwamnati dana ‘yan sanda da kuma na asibiti wadanda suka yi Magana da manema labarai amma basu yada a ambaci sunan su ba don ba a basu damar suyi Magana da manema labarai ba, ammasunce abubuwan fashewar sun kashe mutane 3 kana wasu 10 sun samu rauni a wata kasuwar da tayi fice dake unguwar Shaab, Arewacin birnin na Bagaddaza.

Wannan harin na ranar jiya Lahadi yazo ne kwana daya bayan da wani dan kunar bakin wake na kungiyar ISIS ya auna wani wurin taimaka wa mahajittan Shi’ete, wanda hakan kuma yayi dalilin mutuwar mutane 7 kana wasu 20 suka samu rauni daban-daban.

Sai dai kawo yanzu ba wani ko wasu da suka dauki alhakin aikata wannan danyen aikin na jiya lahadi, sai dai sau tari yan tsananin kishin addinin Sunni suna yawan kaiwa ‘yan Shi’te din kasar ta Iraqi hari, wadanda suke musu kallokn masu aikata sabon da ya cancanta a yanke musu hukuncin kissa.

XS
SM
MD
LG