Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19: Gwamnatin Jihar Lagos Za Ta Bude Wuraren Ibada


Jami'an Gano Masu COVID-19 a Lagos
Jami'an Gano Masu COVID-19 a Lagos

Gwamnan jihar Lagos ya sanar da cewa za a bude Majami’u da Masallatai don jama’a su je yin ibada daga ranar 7 ga watan Agusta, ya yi wannan bayanin ne a wurin wani taron manema labarai a ranar Asabar 1 ga watan Agusta, a cewar wani rahoto na kamfanin dillancin labaran Reuters.

Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya kuma ce za a ba wuraren saida abinci, wuraren rawa da wuraren shakatawa damar sake bude harkokinsu amma ba kamar da ba daga ranar 14 ga watan Agusta, a yayin da jihar inda cutar COVID-19 ta fi kamari ke sassauta matakan kulle da takaita zirga-zirga duk da cewa ana ci gaba da samun karin adadin wadanda ke kamuwa da cutar.

Jihar Lagos, da ke da yawan al’umma miliyan 20, ta samu adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus sama da 15,000 kuma mutum 192 suka mutu, nesa ba kusa ba ita ce jihar da ke da kaso mai yawa cikin mutum 43,537 da suka kamu da cutar a Najeriya.

Gwamnatin jihar ta bada umurnin a rufe wurare da yawa tare da daukar matakan kulle a watan Maris da ya gabata don dakile cutar mai yaduwa da sauri.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG