Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Gangan Wasu Gwamnonin Najeriya Suke Kin Biyan Albashin Ma'aikatanssu


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari
Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Ba wani sabon labari ba ne batun rashin biyan ma'aikata a wasu jihohin Najeriya amma abun dake sabo shi ne batun makudan kudade da gwamnatin tarayyar Najeriya ta rabawa jihohi kimanin Nera biliyan dari biyar da ishirin da biyu da miliyan saba'in da hudu da aka samu daga bashin kasashen waje da aka biya fiye da kima.

Tun farko dai Sanata Dino Melaye yace gwamnatin Buhari ta rabawa jihohi makudan kudade da suka kai dalar Amurka biliyan hudu.

Jihar da ta samu kaso mafi kankanci ita ce jihar Nasarawa wadda ta samu Nera biliyan sittin da takwas. Melaye ya zargi jihohin da cewa basa son kungiyoyin kwadago su san labarin domin kada su matsa lamba sai an biya bashin albashin da ma'aikatan ke bi.

A firarsa ta karshen shekara Shugaba Buhari ya nuna damuwarsa kan albashin ma'aikatan jihohi. Yace jihohi 27 cikin 36 basu iya biyan albashin ma'aikatansu ba, musamman kananan ma'aikata. Yace alhali kuwa da albashin suka dogara su biya kudin haya su kuma rike iyalansu. Yace ga kudin da ake samu amma ba'a yi tanadin komi ba. Ba'a yi tanadin kudin ba. Ba'a gyara wuta ba ko hanyoyi ko kuma layin dogo. Inji Buhari kullum zama a keyi ana watanda da dukiyar jama'a. Yace irin wannan cin amana ba zai dore ba.

Kwararre kan shige da ficen kudi Nuhu Usman yace gwamnoni basa son biyan kudin ne domin yin anfani dasu ta wata hanya daban. Yace lokacin da gwamnatin tarayya ta ba jihohi tallafi ba'a yi wani abu ba sai a wannan karon da Sanata Dino Melaye ya fito ya ballasa abun da gwamnatin tarayya ta rabawa jihohin. Nufin shugaban kasa ne gwamnonin su biya ma'aikatansu kamar yadda shi ya yi a tarayya har da biyan kudin fansho na wajen watanni 18.

Wasu gwamnonin na ganin su ba zasu biya miliyoyin da ma'aikata ke binsu ba. Misali gwamnan jihar Imo cewa yayi ma'aikata su yi aikin kwana uku kawai kowane mako sauran kwanakin kuma duk su tafi gona.

Kwamishanan labaran jihar Gombe Umar Ahmed Suleiman yace matukar gwamna nada niyya zai iya biyan albashin ma'aikatansa kamar yadda yace ma'aikatan jiharsa na samun albashi kan kari. Yace gwamnan jihar abun da ya sa gaba shi ne biyan hakkin ma'aikatansa. Da zara ya samu kudi zai fara cire albashin ma'aikata ne.

Kungiyar kwadagon Najeriya ta bakin Nuhu Toro tace zata dauki mataki kan jihohin da suka gaza biyan akbashin.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

XS
SM
MD
LG