Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilin Da Ya Sa Facebook Ya Sallami Ma’aikata Sama Da Dubu Goma

FILE - A car passes Facebook's new Meta logo on a sign at the company headquarters on Oct. 28, 2021, in Menlo Park, Calif. Facebook parent Meta is laying off 13% of its employees as it contends with faltering revenue and broader tech industry woes.

Wani babban al’amari da har ila yau ya sa kudaden da kamfanin yake kashewa ya karu shi ne, shirin nan na Metaverse da ya tsunduma kansa a ciki, wanda yake cin makudan kudade.

A ranar Larabar da ta gabata, Meta, kamfanin da ya mallaki Facebook, ya sallami ma’aikatansa 11,000 – wato kashi 13 na daukacin ma’aikatansa.

Shugaban kamfanin Mark Zuckerberg ne ya bayyana daukan wannan mataki a wata sanarwa da ya fitar.

Kamfanin ya kuma dakatar da daukan sabbin ma’aikata kamar yadda rahotanni suka nuna.

Tun gabanin sanar da korar ma’aikatan, kamfanin na Facebook ya rage wasu alawu-alawus da garabasa da yake bai wa daukacin ma’aikatansa, kamar na yin wanki kyauta da kai abinci wa iyalansu kyauta.

Rahotannin sun yi nuni da cewa, kamfanin ya dauki matakin ne saboda karuwar da kudaden da kamfanin ke kashewa suka yi da kuma raguwar kudaden shiga.

Bayanai sun yi nuni da cewa, a lokacin ganiyar annobar COVID-19, jama’a na zaune a gida, lamarin da ya sa kamfanonin yanar gizo irinsu su Facebook suka ci kasuwa, amma yanzu al’amura sun sauya saboda an dawo da harkokin yau da kullum.

Hakan ya sa kudaden shigar kamfanin suka ragu matuka.

Baya ga haka, kamfanin na fuskantar barazanar gogayya da sabbin kamfanoni irinsu TikTok.

Wani babban al’amari da har ila yau ya sa kudaden da kamfanin yake kashewa ya karu shi ne, shirin nan na Metaverse da ya tsunduma kansa a ciki, wanda yake cin makudan kudade.

Rahotannin sun yi nuni da cewa, masu hannayen jari a kamfanin na Facebook, sun nuna rashin gamsuwa kan yadda ake kashe kudade a fannin na metaverse.

Metaverse, shiri ne da kamfanin na Meta ya dukufa akai, wanda ke muradin ganin an fadada fasahar sadarwa ta zamani ta yadda za a samu bunkasa a fannin cudanya, kasuwanci da alaka a kafar yanar gizo a duniya.

XS
SM
MD
LG