Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Najeriya Ya Kafa Tarihin Yin Wasan Dara Tsawon Sa’o’i 60 A Jere


Tunde Onakoya
Tunde Onakoya

Onakoya ya shafe sa’o’i 60 a jere yana wasan darar chess ba tare da an yi galaba akansa ba tun daga karfe 10 na safiyar 17 har izuwa karfe 11 da rabi na daren 19 ga watan Afrilun da muke ciki a dandalin “Times Square” dake birnin New York na kasar Amurka.

NEW YORK - Wani zakaran darar chess kuma mai fafutukar koyar da yara ilimin yara dan Najeriya mai suna Tunde Onakoya ya kafa tarihin shiga cikin kundin bajinta na duniya a wasan dara.

Onakoya ya shafe sa’o’i 60 a jere yana wasan darar chess ba tare da an yi galaba akansa ba tun daga karfe 10 na safiyar 17 har izuwa karfe 11 da rabi na daren 19 ga watan Afrilun da muke ciki a dandalin “Times Square” dake birnin New York na kasar Amurka.

A cewar Tunde Onakoya, “ba kowa ne zai samu damar samun ilmi ba kuma yara da dama na samun mafita ta wasu hanyoyin na daban”.

Ya kara da cewar, kowane nada irin baiwa da basirar da Allah ya bashi kuma darar chess wata hanya ce mai sauki ta zakulo wannan basira.

Tunde Onakoya
Tunde Onakoya

Babban burinsa shine raba gudunmowar kayan darar chess guda milyan 1 a fadin duniya. Kuma izuwa yanzu ya nasarar raba kayan darar guda dubu dari da sha shida (116, 000) a kasashen duniya 25.

Haka kuma zai yi amfani da wannan dama wajen tara dala miliyan guda domin gina makarantar koyan darar chess kyauta da kuma dakin bincken kirkire-kirkire a jihar Legas.

Masu rike da kambun bajintar darar chess mafi tsayi kafin Onakoya, sune Hallvaed Haug da Sjur Ferkinstad daga kasar Norway da suka shafe tsawon sa’o’i 56 da mintuna 9 da dakikoki 37 suna wasan.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG