Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar hadin kan Afrika ta jinkirta tuhumar shugaban kasar Sudan


Shugaban kasar Sudan Omar Hassan al-Bashir (hoto daga runbun hotuna)
Shugaban kasar Sudan Omar Hassan al-Bashir (hoto daga runbun hotuna)

Kungiyar Hadin kan Afrika ta bukaci Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya jinkirta tuhumar Shugaban kasar Sudan Umar al-Bashir.

Kungiyar Hadin kan kashen nahiyar Afrika ta bukaci Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya jinkirta tuhumar shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir, wanda yake fuskanta sammacen kasa da kasa bisa zargin aikata laifukan yaki. Shugaban kasar Malawi Bingu wa Mutharika ya bayyana a taron kolin Majalisar Dinkin Duniya cewa, sammacen zai iya kawo cikas a yunkurin wanzar da zaman lafiya. Ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya tayi amfani da karfin ikonta wajen dakatar da yunkurin gurfanar da shi gaban kotu na tsawon shekara guda, domin bada damar ci gaba da tattaunawa ba tare da wani cikas ba. Mr. Bashir yana fuskantar tuhumar kotun bin kadin laifuka ta kasa da kasa bisa zargin kulla makarkashiyar yiwa mata fyade, da kisan kai, da aikata sauran miyagun laifuka kan farin kaya a yankin Darfur na yammacin Sudan. Ya kubuta daga kamu, duk da yake ya sha tafiya kasashen da suka amince da ikon kotun kasa da kasar. Kwanan nan ya tafiya kasar Kenya inda ya halarci bukin sa hannu a sabon kundin tsarin mulkin kasar.

XS
SM
MD
LG