Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Donald Trump: Kudirin Shafewa Da Maye Gurbin Tsarin Kiwon Lafiya Na Obama Ya Wargaje


An bayyana cewa Shugaba Donald Trump, na shirin mikewa a wannan satin, bayan ya fuskanci koma baya mafi muni a jaririyar gwamnatinsa a makon jiya.

A daidai lokacin da kunnuwan masu zabe ke cike da muryar nan mai cewa "Za mu shafe mu kuma maye gurbin tsarin kiwon lafiya na Obama" sai kawai wannan mashahurin alkawarin da Trump, ya yi ta yi lokacin yakin neman zabe ya wargaje, bayan da 'yan Republican masu rinjaye a Majalisa su ka kasa daukar mataki na farko a majalisance, na samar da madadin tsarin saukaka jinyar da Obama ya bullo da ita.

"Na yi takaici," a cewar Shugaban kasar a ranar Jumma'a bayan da ta bayyana karara cewa ba za a samu isassun kuru'u daga 'yan Republican don gabatar da kudurin doka na maye gurbin ba. Ya kara da cewa, "abin ya dan bani mamaki, in gaya maku gaskiya. Al'amari ne da bai fi karfinmu ba. Saura kiris fa mu ida shi."

Amma zuwa jiya Lahadi, sai Trump, ya bayyana fushinsa ta kafar Twitter, ya na mai tura laifin ga wasu kungiyoyin rikau na Republican, wadanda su ka zake cewa kar a amince da kudurin dokar.

Shugaba Trump,ya rubuta ta kafar Twitter cewa, "'Yan jam'iyyar Democrats, na ta dariya a Washington cewa Kungiyar Freedom Caucus tare da taimakon kungiyar Club for Growth and Heritage, sun ceci cibiyar tsarin iyali da kuma tsarin kiwon lafiya na Obama!".

Da ya ke magana a kafar labarai ta FOX NEWS, Shugaban Ma'aikata na Fadar White House Reince Priebus, ya yi watsi da rahotannin labarai da ke nuna cewa Shugaba Trump, ya tura laifi kan shi Priebus, da Kakakin Majalisar Wakilai Paul Ryan, game da wannan shan kayen. "Ni ba na wani cikin tashin hankali." "Wannan rade-radin aikin magulmata ne kawai," abin da ya gaya ma Chris Wallace, kenan mai shirya shirin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG