Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Donald Trump Ya Nada Shugaban Ma’aikatar Tsaron Amurka


Jim kadan bayan rantsar da Donald Trump a matsayin sabon shugaban kasar Amurka na 45, Trump ya rattaba hannu kan wasu takardu da a hukumance suka tabbatar da shi a matsayin shugaban kasa.

Haka kuma, Trump ya rattabawa wata takarda hannu da take nufin Janal James Mattis mai ritaya, ya zamanto shugaban ma’aikatar tsaron Amurka. Shi dai Mattis yayi ritaya ne shekaru uku da rabi da suka gabata, bayan kwashe sama da shekaru 40 yana aiki da sojin Amurka, a cewar mai magana da yawun fadar White House, Sean Spicer.

Wata kudurin doka da akayi tun alif 947 kan tsaron ‘kasa, ta bukaci duk wani da yayi aikin soja sai ya kwashe shekaru bakwai kafin karbar wani mukami daga ‘yan siyasa.

A makon da ya gabata ne ‘yan Majalisar Amurka suka baiwa Mattis damar karbar wannan mukami, wanda zai bashi damar shugabantar ma’aikatar tsaro ta Pentagon duk da cewar yayi ritaya ne daga rundunar sojan ruwa a shekara ta 2013.

Shugaban ya rattaba hannu kan takardar ne a lokacin da yake tare shugaban ‘yan Majalisar Republican, da kuma shugabar marasa rinjaye a Majalisar wakilai Nancy Polosi da kuma ‘ya ‘yansa da jikokinsa.

XS
SM
MD
LG