Shugaban kungiyar hadin kan kirista wato CAN, reshen jahar Pilato, Rabaran Fada Polycap Lubo yace, ya kamata matasan su baiwa gwamnati damar duba bukatun da suka gabatar mata.
Mai martaba Sarkin Wase, Alhaji Muhammadu Sambo Haruna, yace, tilas ne hukumomi su zauna da masu tada hankalin don samun masalaha.
Komishinan yada labarai da sadarwa a jahar Pilato, Dan Manjang, a nasa bangaren ya yi kira ga jama’a da su yi hakuri da juna domin samun dawwamamman zaman lafiya.
Rundunar tsaro ta STF a jahar Pilato, ita kuma tace ta kame mutane fiye da dari uku da ake zarginsu da fasa rumbuna, ofisoshin gwamnati da gidajen wasu mutane a jihar da zimmar kwashe musu kadarori a matsayin ganima.
Saurari cikakken rahoton Zainab Babaji cikin sauti:
Facebook Forum