Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Neja Ta Kafa Cibiyoyin Tantance Cutar Ebola


Dr. Babangida Aliyu gwamnan jihar Neja
Dr. Babangida Aliyu gwamnan jihar Neja

A cigaba da kokarin yaki da cutar ebola da ta zama wata sabuwar annoba a wasu kasashen yammacin Afirka, gwamnatin jihar Neja ware wasu cibiyoyi guda shida domin tantance cutar ebola.

A wani taron manema labarai kwamishaniyar kiwon lafiya ta jihar Hajiya Hadiza Abdullahi ta bayyana inda cibiyoyin suke.

Tace sun ware wurare shida tun kafin ma cutar ta shigo jihar. A karamar hukumar Borgu sun ware guda daya. Akwai daya a Shiroro. Akwai daya kuma a Jaji cikin Mokwa.

Idan har lamura suka yi muni za'a bude daya a Kontagora, daya a Lahun daya kuma a Suleja. Gwamnati ta bada kwangilar sayen kayan sawa na musamman da ake bukata kafin a ga mai cutar ebola.

A halin da ake ciki majalisar limaman masallatan Juma'a da gwamnati tace zata nemi hadin kai da su domin sanin abun da ya kashe mutum kafin a yi masa jana'iza, sun bayyana matsayinsu akan lamarin. Imam Umar Faruk sakataren majalisar limaman yace a shariar musulunci ba'a yadda ba maiwanke gawa ya tabata da yatsunsa. Akwai abun da ake sawa kafin safar hannu ta roba ta fito. Yanzu da aka samu safar duk limamai masu wanke gawa sai sun yi anfani da safar hannun. Tantance gawa babu laifi idan an iya ganewa. Amma ba zasu yadda da kona gawar musulmi ba wai domin hana yaduwar cutar.

Ma'aikatar kiwon lafiya ta karyata wani rahoto dake cewa cutar ta shigo jihar ta Jamhuriyar Benin.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:55 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG