Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Zata Dauki Sabbin Matakan Dakile Boko Haram- Mansur Dan Ali


Janar Mansur Dan Ali, Ministan Tsaron Najeriya
Janar Mansur Dan Ali, Ministan Tsaron Najeriya

Biyo bayan harin bamabamai da yunkurin kutsawa cikin birnin Maiduguri da 'yan kungiyar Boko Haram suka yi jiya wanda ya lakume rayuka 14 tare da raunata wasu da dama, gwamnati ta kuduri aniyar daukan sabbin matakan dakile duk wani yunkurin 'yan ta'addan

Gwamnatin tarayyar Najeriya da jami'an tsaron kasar sun sha alwashin daukan sabbin matakan durkushe duk wani yunkurin samame da kungiyar Boko Haram zata shirya yi a kowane sashen kasar.

Ministan tsaro Janar Mansur Dan Ali mai ritaya shi ya bayyanawa Muryar Amurka hakan biyo bayan harin ba zata da kungiyar Boko Haram ta kai Maiduguri jiya.

Ministan yana mai cewa kowane lokaci 'yan ta'addan na neman suyi farfagandar nuwa duniya har yanzu akwaisu. Yace farmakin da suka kai na bazata ne kuma yana iya faruwa koyaushe amma idan mutane suna tseguntawa jami'an tsaro abubuwan dake faruwa nan da nan za'a katsesu.

Dangane da farmakin jiya ministan yace nan take aka gama dasu. Babu wanda ya samu shiga birnin Maidugurin. Yace babu yadda za'a yi a samu jami'an tsaro koina. Amma mutanen dake wurin su ne zasu dinga taimakawa da bayanai da.

Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:28 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG