Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Zata Gudanar da Bincike Akan Yunkurin Raba Kasar


Taron Majalisar Zartaswa, yau a Abuja
Taron Majalisar Zartaswa, yau a Abuja

Gwamnatin tarayar Najeriya ta zabura domin ta tunkari yawan kiraye kirayen a bara kasar da 'yan asalin kabilar Igbo suka fara yi sai kuma ga matasan arewa suna kiran mutanen Igbon su fice daga jihohin arewa nan da wata uku saboda wai sun gaji da zaman raini da rashin ya kamata da Igb ke nunawa 'yan arewa.

Yau a taron majalisar zartaswar tarayyar Najeriya a karkashin shugabancin mukaddashin shugaban kasa Farfasa Yemi Osinbajo, gwamnati ta umurci mai ba shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro, Janar Muhammad Mongunu, da ya gudanar da cikakken bincike akan yunkurin raba Najeriya da wasu keyi.

Kwna kwanan nan 'yan kabilar Igbo suka tashi haikan suna neman su kafa tasu kasar da suka kira Biafra, sai kuma jiya wasu matasan arewa suka ba Igbo wa'adin watanni uku da su fice daga jihohin arewa su ma 'yan arewan dake kasar Igbo su koma gida a raba gari kowa ya kama tasa hanyar.

Wannan matsayin matasan arewacin Najeriya ya zo da bazata saboda shi ne karon farko da kungiyoyin suka hada kai har ma suka bada wa'adi cewa wata al'umma ta bar Najeriya yayinda suke ikirarin cewa 'yan arewa sun gaji da kasancewa cikin kasa daya da al'ummar Igbo.

Malam Garba Shehu kakakin fadar shugaban kasar Najeriya ya bada karin haske akan umurnin da gwamnati ta bada. Yana mai cewa maganar ta taso a taron majalisar ministoci. An lura cewa manyan maganganu suna fitowa daga bakin mutanen da ake cewa matasa ne. Sun nemi gwamnati tayi hattara domin kada a yi sakaci lamarin ya fi karfin kasar. Dalili ke nan da suka kira mai ba gwamnati shawara akan harkokin tsaro ya binciki lamarin domin a san matakin da za'a dauka.

Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:17 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG