Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hafsohin Sojan Najeriya Sun Tsallake Rijiya Da Baya A Hannun 'Yan Boko Haram


Birgediya janar Victor Ezugu da Manjo janar I M Alkali
Birgediya janar Victor Ezugu da Manjo janar I M Alkali

'Yan Kungiyar Boko Haram sun dana tarko amma bai kama ba.

Babban hafsan mulki na rundunar sojan kasa ta Najeriya, manjo janar I M Alkali da babban kwamandan shiyya ta 7 ta sojojin kasa, Birgediya janar Victor Ezugu, sun tsallake rijiya da baya a lokacin da suke kan hanyar zuwa Pulka.
'Yan kungiyar boko haram sun binne Bama bamai hudu a kusa da mararrabar Banki wanda naurorin sojojin suka gano aka kuma samu nasarar tonowa da tarwatsawa.
Hafsoshin na kan hanyarsu ne na bibiyar dakarun runduna na ashirin da shida (26), da aka tura aikin Operation Lafiya Dole domin fafatawa da 'yan Boko Haram.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG