Hukumar Hisbah a Kano ta yi nasarar dakile auren da aka shirya daurawa a tsakanin, Mujahid da Abba wadan da ake zargin cewa 'yan daudu ne.
Hukumar ta Hisbah ta ce ta gono shirin bikin auren ne, wanda a ka shirya yi da daren jiya, a wani gida mai suna Event Center da ke bayan Dogon Banki a birnin Kano.
'Yan Dokar Hukumar Hisbah sun sami Nasarar kama yan mata 15 da samari 4 ciki, har da mai wurin na Event Center, da wata budurwa Mai suna Salma wacce ake zargi da yinkurin sakaya ainihin manufar bikin domin ya yi kama da bikin birthday.
Da ya ke Ganawa da 'yan mata da dakarun Hisbah su ka kamo, Babban Kwamandan Hukumar ta Hisbah, Dr. Harun Muhammad Sani Ibin Sina, ya yi magana dangane da yadda iyaye ke yin wasarere da amanar da Allah ya aanka wajen kula da yi ma ya ya tarbiyya.
Babban kwamandan hukumar ta Hisbah ya ba da umurnin da a gayyato iyaye ko makusantan wadannan 'yan mata masu karancin shekaru, wadanda aka Kamo, domin sanar da su halin da yayansu ke ciki.
Hukumar ta ce zata dauki matakin ladabtar da masu gidan Event Center domin su girbi abinda su ka shuka.
Ibin Sina ya ce duk da rashin nasarar kamo 'yan daudun, wadan da su ka shirya yin auren a tsakaninsu, ya ce dakarun Hisbah za su ci gaba da sa ido har sai an kai ga nasarar da ake so na dakile dukkan nau'ukan aikata badala a jihar kano.
Saurari cikakken rahoton Baraka Bashir: