Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Da Falasdinawa Za Su Fara Tattaunawa Yau Alhamis


Shugaba Obama yace gurin shawarwarin shi ne cimma daidaituwa a kan dukkan batutuwa na cikakkiyar makomar bangarorin da aka ajiye sai karshe

Shugaba Barack Obama yace tilas ne Isra'ila da Falasdinawa su rungumi wannan dama ta cimma zaman lafiya mai dorewa a sanadin komawa ga tattaunawa kai tsaye a tsakaninsu. Mr. Obama ya zauna ya tattauna da firayim ministan bani Isra'ila, Benjamin Netanyahu, da shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas da wasu shugabannin na Gabas ta Tsakiya kafin bude shawarwarin da za a yi yau alhamis a ma'aikatar harkokin wajen Amurka.

Daya bayan daya, shugaban na Amurka yayi marhabin da shugabannin Isra'ila da na Fasldinu da na Jordan da kuma Masar a ofishinsa a fadar White House. Wannan shi ne karon farko da Mr. Obama ya tsunduma kansa gadan-gadan a yunkurin warware batutuwan da suka gagari shugabannin Amurka na baya.

Shugaba Obama yace gurin shawarwarin shi ne cimma daidaituwa a kan dukkan batutuwa na cikakkiyar makomar bangarorin da aka ajiye sai karshe, da kuma tattauna da zata kai ga samun 'yantacciyar kasar Falasdinu mai diyauci da bin tafarkin dimokuradiyya wadda zata yi zaman lumana a gefen kasar yahudawa ta Isra'ila.

Idan har sassan ba su rungumi wannan tattaunawa tsakani da Allah ba, shugaban yace wannan rikicin Isra'ila da Falasdinawa zai ci gaba da addabar 'ya'ya da jikoki.

Yau alhamis, sakatariyar harkokin wajen Amjurka Hillary Clinton zata bude shawarwarin, daga nan kuma firayim minista Benjamin Netanyahu na Isra'ila da shugaban Falasdinawa nMahmoud Abbas zasu yi jawabai kafin a shiga ciki a fara tattaunawa. Wakilin Amurka a Gabvas ta Tsakiya, George Mitchell zai yi jawabi ga 'yan jarida daga bisani.

XS
SM
MD
LG