Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jakadan Faransa Da Ya Bar Nijar Ya Fasa Kwai Game Da Juyin Mulkin Kasar


Shugaban kasar Emmanuel Macron
Shugaban kasar Emmanuel Macron

Wani bahasin da Jakadan Faransa Sylvain Itte ya gabatar a Majalissar Dokokin Kasar ta Faransa sun farfado da mahawara dangane da irin rawar da ake zargin tsohon Shugaban kasar Nijar Issouhou Mahamadou ya taka a juyin mulkin da soja suka yi wa Shugaba Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan Yulin 2023.

WASHINGTON, D. C. - Jakadan wanda sojojin juyin mulkin suka kora daga Nijar a watan Satumba da ya gabata ya ce ya dogara akan wasu kwararan hujojoji dake tabbatar masa cewa biri ya yi kama da mutun sai dai wasu ‘yan Nijar din na nuna rashin gamsuwa da bayanan jakadan.

A zaman da kwamitin tsaron majalissar dokokin Faransa ya gudanar a asirce ne jakadan Faransa wanda hukumomin mulkin sojan CNSP suka kora daga kasar, Sylvain Itte, ya amsa tambayoyi game da zahirin abubuwan da ya sani dangane da koma bayan diflomasiyar da Faransa ta fuskanta a kasar musamman daga ranar da soja suka kifar da gwmnatin Mohamed Bazoum.

Sylvain Itte ya jaddada zargin tsohon Shugaban Nijar, Mahamadou Issouhou, da hannu a juyin mulkin 26 ga watan Yuli.

‘Dan jaridar kasa da kasa mazaunin Faransa, Dr. Seidick Abba ya karanta rahoton zaman majalissar da sai a wannan makon ya fito fili.

Sabani kan batun gudanar da harkokin man fetur a wani lokacin da kasar ke dab da soma fitar da shi zuwa kasuwannin duniya da maganar yaki da cin hanci wanda hambararriyar gwamnatin ta sa gaba na daga cikin dalilan da Sylvain Itte ya ayyana a matsayin mafarin wannan juyi.

Jagoran kungiyoyin Reseau Esperance, Bachar Mahaman, na ganin bukatar daukan zarge-zagen jakadan da mahimmanci.

Sai dai daya daga cikin jagororin kungiyoyin fafutikar kin jinin siyasar Faransa a Afirka kuma mamba a kungiyoyin Front Patriotique masu goyon bayan hukumomin CNSP, Bana Ibrahim, ya ce akwai bukatar taka-tsan-tsan kan furicin na mutumin da aka yi watsi baram-baran a tsakaninsa da mahukuntan Nijar.

Sake farfado da zargin hannun Mahamadou Issouhou wajen kifar da abokin tafiyarsa na shekaru sama da 30 na zuwa a wani lokacin da wasu rahotanni ke cewa tsohon shugaban kasar ta Nijar ya tafi kasar Habasha a cikin daren Laraba da nufin halartar taron ZLECAF ko AfCTA .

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Jakadan Faransa Da Ya Bar Kasar Ya Fasa Kwai Game Da Juyin Mulkin Nijar .MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:36 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG