Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam’iyyar APC Ta Dakatar Da Shugabanta Na Kasa Ganduje


Abdullahi Umar Ganduje (Facebook/Gwamnatin Kano)
Abdullahi Umar Ganduje (Facebook/Gwamnatin Kano)

Mambobin jam’iyyar APC na mazabar Ganduje da ke karamar hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje.

WASHINGTON, D. C. - Majalisar zartaswa ta mazabar Ganduje karkashin jagorancin Haruna Gwanjo ne suka bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Kano ranar Litinin.

Gwanjo ya ce dole ne tsohon gwamnan ya wanke sunansa daga zarge-zargen cin hanci da rashawa dangane da shari’ar dala da ta dade.

Wani faifan bidiyo da aka yada ya nuna hoton Ganduje da ake zargin yana karbar wasu makudan kudaden daloli yana cusa su a aljihun rigar sa, a matsayin cin hanci daga wani mutum da aka ce ‘dan kwangila ne.

Bidiyon, wanda ya jawo hankalin jama'a sosai a shekarar 2017, ya kasance abin dubawa sosai.

Ganduje dai ya musanta abin da faifan bidiyon ya kunsa a lokacin da ya fara bayyana tare da tabbatar da cewa ba shi da wani laifi, amma bayan shekaru da dama gwamnatin Gwamna Abba Yusuf ta jam’iyyar NNPP ta sake duba lamarin, inda ta sha alwashin gurfanar da tsohon gwamnan a gaban kuliya.

Babbar kotun jihar Kano za ta gurfanar da Ganduje a ranar Laraba 17 ga Afrilun 2024, kan zargin karbar rashawa da karkatar da kudade da kuma almubazzaranci, ciki har da zargin karbar cin hancin dala 413,000 da kuma Naira Biliyan 1.38.

Babban Lauyan Jihar Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Haruna Dederi, ya ce za a gurfanar da Ganduje ne tare da matarsa da wasu mutane shida.

Gwamnatin Yusuf, wacce ta fara tuhumar mutane takwas da ake kara, ta bayyana shirinta na gabatar da shaidu 15 da za su bayar da shaida a gaban mai shari’a Usman Na’aba na babbar kotun jihar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG