Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyar UDR Tabbat ta kasar Niger ta maida martani


Mahamadou Issoufou, shugaban kasar Niger
Mahamadou Issoufou, shugaban kasar Niger

Jam’iyar UDR Tabbat ta jamhuriyar Niger ta maida martani akan matakin korar ‘yan jam’iyar daga gwamnatin shugaba Yusufu Mahammadu ba tare da an shawarci shugabannin jam’iyar ba.

Jam’iyar UDR Tabbat ta jamhuriyar Niger ta maida martani akan matakin korar ‘yan jam’iyar daga gwamnatin shugaba Yusufu Mahammadu ba tare da an shawarci shugabannin jam’iyar ba.

Jam'iyar ta yi wannan korafi ne a karshen wani taron da ta gudanar aranar Asabar da yamma a birnin Niamey.

Wannan shi ne karon farko da jam’iyar ta UDR Tabbat ke bayyana matsayinta a fili tun bayanda shugaban kasar Nijer Mammadou Youfou ya kawo karshen aikin kusoshin dake wakiltar ta a cikin gwamnati cikinsu har da shugaban jam’iyar na kasa Amadu Bubakar Cisse .

Magatakardan wannan jam’iya Alhaji Abdu Bukari yace matakin ya zo masu da bazata saboda ba a tuntubesu ba kafin a yanke wannan shawara.

Da yake maida martani kan wannan korafi na rashin shawara , shi kuma Alhaji Asumana Mahammadu wani kusa a kwancen jam’iyun MRN ya ce duk da faruwar wannan al’amari da wasu ke dauka tamkar wulakanta jam’iyar ne da shugabannin ta, Malama Rabi Arzika ta jam’iyar UDR Tabbat ta ce har kwanan gobe suna cikin kawancen jam’iyun MRN mai jan ragamar mulkin Nijer.

Masu lura da al’amuran siyasar Nijer na ganin akwai yiyuwar nan gaba baraka ta kunno kai a tsakanin ‘yayan Udr Tabbat bisa la’akari da cewa wani jigon jam’iyar ne ya canji Usman Abdu a mukamin ministan raya al’adun kasa ba tare da samun izinin kwamitin kolin jam’iyar ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00

XS
SM
MD
LG