Yawan samun laifukan kisa na dadda tada hankalin al’ummar yankın arewacin Najeriya.
A wannnan Shekarar da aka yi bankwana da ita ta ne wata matar aure, Hafsa Surajo, ta kashe abokin sana’arta ta hanyar caccaka masa wuka, al'ammarin da ya ja hankalin jama’a.
Wannan shine karo na biyar da samun irin wannan kısa mai tada hankali a yankın na Arewacin Najeriya
Idan za’a iya tunawa a Nuwamban 2017 aka zargi Maryam Sanda da laifin kashe mijinta mai suna Bilyaminu Bello, wanda da ne ga tsohon shugaban jam'iyyar PDP, Bello Halliru Mohammad.
Rahotanni a lokacin da al'amarin ya faru sun ce Maryam ta samu sabani da mijin nata ne wanda hakan ya kai ga ta caka masa wuka.
An gurfanar da ita tare da yanke mata hukuncin kisa a shekarar 2020 bayan samunta da laifin kashe mijinta.
Haka kuma wata mahaifiyar da ta kashe ‘ya'yanta biyu a Kano a watan Oktoban 2020 inda aka shiga wani hali na ruɗu a birnin Kano, bayan da aka yi zargin uwar ta kashe a Unguwar Sagagi.
Haka kuma Kisan Hanifa, yarinya mai shekaru biyar a Kano, ya tayar da hankalin jama’a sakamakon yadda lamarin ya faru cike da tausayi da takaici.
An yankewa malaminta Abdulmalik Tanko hukuncin kisa bayan samunsa da laifin garkuwa da Hanifa da laifin kisanta shima shiru har yanzu ba’a aiwatar da hukuncin ba.
Kazalika a shekarar 2022 ne aka zargi wani dan kasar China mai suna Geng Quangron da kashe budurwarsa mai suna Ummulkulsum Sani Buhari wadda aka fi sani da Ummita.
Shi ma wannan lamarin ya tayar da kura kasancewa yadda ya aikata laifin kisan sakamakon ba dan Najeriya ba ne
An zargi dan kasar Chinan da bin Ummita har gidansu da ke unguwar Janbulo inda ya soka mata wuka har ya yi ajalinta.
Ko me ke haifar da yawa yawan kisan kai da mata, wasu lokutan ma maza, ke yi ?
Wakiliyar Muryar Amurka, Baraka Bashir ta shiga gari ta bincika, kuma ga rahoton da hado.
Dandalin Mu Tattauna