Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jihar Neja Ta Dakatar Da Wasu Shugabannin Kananan Hukumomi


Gwamnan Jihar Neja Dr. Babangida Aliyu
Gwamnan Jihar Neja Dr. Babangida Aliyu

Gwamnatin Jihar Neja ta dakatar da wasu shugabannin kananan hukumomi sabili da karkata kudaden gwamnati zuwa wani wuri daban.

Gwamnatin Jihar Neja ta dakatar da wasu shugabannin kananan hukumomi saboda yin sama da zargin yin sama da fadi da wasu makudan kudaden da za'a yi aiki da su na inganta rayuwar jama'arsu.

Sanarwar dakatar da shugabannin ta fito ne daga mataimakin gwamnan jihar Alhaji Ahmed Musa Ibeto.Wadanda aka dakatar su ne Peter Pius na karamar hukumar Rafi da Alhaji Saidu Pisa na karamar hukumar Borgu. Mataimakin gwamnan jihar ya shaidawa manema labaru cewa an dakatar da wadannan zababbun shugabannin ne saboda koke-koke da suka samu daga kansilolin hukumomin.

Dakatawar ta wata uku ce bisa ga doka domin a yi bincike. Alhaji Ahmed Musa Ibeto ya ce bai kamata a ce ana bincike su kuma shugabannin suna cigaba da zama kan kujerunsu na milki. Da aka tambayeshi ko matakin da gwamnati ta dauka yana da nasaba da siyasa sai ya ce babu siyasa ciki domin shugabannin biyu duk 'yan jam'iyyarsu ce ta PDP. Ya kara da cewa gwamnatinsu tana son ta nuna wa kowa cewa idan mutum ya yi laifi za'a hukuntashi ko daga wace jam'iyya ya fito.

Kansilolin karamar hukumar Rafi sun zargi Peter Pius da sayar da tiransfamomin wutar lantarki har sama da guda goma. Wani kansilo daga karamar hukumar ya ce barnar da a keyi ta yi yawa. Ban da sayar da kayan lantarki ya ce sun bada kwangilar nera miliyan 19 amma Peter Pius sai da ya matsawa dan kwangilan ya karbi cin hancin nera miliyan takwas. Su tiransifamomin an bayar dasu gyara ne a Kano sai Peter Pius ya zaga ya je ya sayar dasu. Kansilo Mohammed Abdullahi Babani ya ce lamarin ne ya yi tsami domin rashin gaskiya da almundahana.

Su ma kansilolin karamar hukumar Borgu sun ce cin kudin ne ya yi yawa. Kansilo Ibrahim Musa Lafiya ya ce abu na bayan nan shi ne cin kudin alhazai wajen nera miliyan 13 da shugaban hukumar Alhaji Saidu Pisa ya yi. Haka ma hukumar wutar lantarki ta biya kudin kasa nera miliyan 44 amma ya ce miliyan hudu suka biya wato ya danne miliyan 40 ke nan. Kansilo Umar S Wakili ya ce dakatar da shugaban hukumarsu ta sa mutanen Borgu suna cikin murna.

Duk kokarin jin ta bakin wadanda aka dakatar ya cutura.Amma wani na hannun daman Peter Pius Audu Gurgu Tegas ya ce idan za'a yiwa al'umma aiki a tsaya a yi. Ya ce a guji zarge-zargen banza. Ya ce kage aka yiwa Peter Pius.

Mustapha Nasiru Batsari nada rahoto.




XS
SM
MD
LG