Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kakakin majalisar dokokin kasar Somaliya ya yi watsi da yunkurin tsige shi


Sharif Hassan Sheikh Adan (file photo)
Sharif Hassan Sheikh Adan (file photo)

Kakakin majalisar dokokin kasar Somaliya yayi watsi da wani yunkurin da aka yi na kawar da shi daga karagar mulki, a rudamin siyasar kasar na baya bayan nan.

Kakakin majalisar dokokin kasar Somaliya yayi watsi da wani yunkurin da aka yi na kawar da shi daga karagar mulki, a rudamin siyasar kasar na baya bayan nan.

Kakakin Sharif Hassan Sheikh Adan ya yi hira da Muryar Amurka kwana daya bayan ba hammata iska da aka yi a dandalin majalisar tsakanin magoya bayanshi da ‘yan hamayya.

Ranar Talata ‘yan majalisar dake adawa da Adan suka kada kuri’ar tsige shi inda mutane dari biyu da tamanin suka amince uku kuma suka nuna kin amincewa.

Adan ya shaidawa Muryar Amurka cewa, kuri’ar bata da tasiri kasancewa yana kasar Italiya a lokacin kada kuri’ar. Ya kuma ce adadin mutanen da suka bayyana kin amincewa da shi bai kai abinda ake yayatawa ba.

Gwamantin wucin gadi ta kasar Somaliya ta shafe shekaru tana fama da fadan cikin gida da ya gurguntar da yunkurin wanzar da zaman lafiya a kasar, inda gwamnati ke gumurzu da mayakan da ake dangantawa da kungiyar al-Qaida.

Wakilan Majalisar wakilan kasar Somaliya, a cikin zauren Majalisar

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG