Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamaru Ta Dauki Matakan Karfafa Tsaro domin Kawar da 'Yan Boko Haram


 Marchin Barga babban sifeton 'yansandan kasar Kamaru
Marchin Barga babban sifeton 'yansandan kasar Kamaru

Yawaitar hare haren da 'yan Boko Haram ke kaiwa kasar Kamaru, musamman a jihohin arewa mai nisa da ta gabashin kasar ya sa ta dauki matakin bi gida gida tana binciken makaman da za ta kwace da hukumta wadanda aka kama dasu

Kwamandan jandarmomin jamhuriyar Kamaru John Baptist Makam ya dauki matakan kara karfafa tsaro a duk fadin kasar.

Kwamandan ya umurci jandarmomin kasar baki daya da su sake jajircewa wajen ganin an zakulo duk wanda ake kyautata zaton yana da hannu a hare-haren da Boko Haram ke yawan kaiwa musamman ma a jihar arewa mai nisa.

Kwamandan yace zasu yi kokari matuka gaya su kare kasarsu daga ayyukan ta'addanci da 'yan ta'addan Boko Haram. A cewarsa yanzu zasu soma shiga gida gida domin zakulo 'yan ta'addan daga inda suke boyewa tare da kama makamai.

Dangane da abun da zasu yi idan har sun kama makamai a gidajen mutane, kwamandan yace zasu mika mutanen ga kotun soja domin yi masu hukumcin da ya dace.

Malam Yau dan kungiyar kare hakkin bil'Adama ya bayyana tsoronsu dangane da binciken gida gida saboda kowane lokaci gwamnatin Kamaru tayi hakan ta kan take hakkin mutane, injishi. Yace suna rokon gwamnati idan ta yi aikin tayi da tsoron Allah tare da kare hakkin mutum.

Ko a karshen makon da ya gabata sai da 'yan ta'adda suka kai hari a wasu kauyukan garin Kwalkwata.

Ga rahoton Muhammad Awal Garba

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:45 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG