JIGAWA, NIGERIA - Tsarin bada rancen wadda ke karkashin Shirin da bankin duniya ya bullo da shi mai lakabin ACReSAL domin tallafawa manoma a kararar kusa da yankin Sahel da nufin dakile mummunan tasirin da sauyin yanayi ke yi ga tsarin noma da kiwo, muhalli da kuma albarkatun ruwa, nada nufin kawo sauyi mai ma’ana ga rayuwar mazauna karkara.
Jihohi 19 na arewacin Najeriya da yankin birnin tarayya Abuja ne za su ci gajiyar wannan Shirin na ACReSAL, amma shi wancan tsari na bada lamuni ga manoma a tafarkin da babu kudin ruwa a ciki.
An zabi jihohin Jigawa da Yobe ne domin kaddamar dashi a matakin gwaji, a cewar Alhaji Shehu Mohammed, Kodinetan dake kula da Shirin ACReSAL a jihar Yobe.
Ya kara da cewa, “Kowace kungiya za’a ba ta dala dubu 25, sai akace ayi gwaji, shine aka zabi jihohi 8 daga cikin 19 na arewa kuma sai aka fara aikin gwajin da jihohin Jigawa da Yobe kuma yanzu haka mun je mun zauna da masu ruwa da tsaki a kananan hukumomin da za’a fara gwajin dasu kuma an kammala dukkanin shirye-shiryen da suka kamata”.
Dr Nura Ibrahim Kazaure dake zaman Kwamishinan Kula da Muhalli da Lamuran Sauyin Yanayi na jihar Jigawa yace gwamnatin jihar na daukar wannan shirin na Bankin Duniya da muhimmancin gaske, yana mai cewa
“Gwamnatin Jigawa tayi fice, har lambar yabo aka bamu a bara, saboda mu kadai ne jihar da suka sanya naira biliyan daya a matsayin namu kason na aiwatar da wannan Shirin kuma a bana ma muna nazarin adadin kudaden daya kamata mu zuba”
Kauyen Gamsarka na yankin karamar hukumar Auyo dana Dabi a karamar hukumar Ringim masu dimbin manoman rani dana damina dukkanin a jihar Jigawa sune za’a fara aiwatar da shirin dasu, kuma Malam Hamisu Mohammed Dabi dake jagorantar daya daga cikin kungiyoyin na cewa,
“An ba mu horo akan dabarun shirya noma na zamani domin riba, an koya mana duk abubuwan da suka kamata mu sani, don haka an sanya mu akan hanyar daya kamata mu bi domin cin gajiyar noma yadda ya kamata, yanzu kawai abin daya rage shine samun kudaden aiwatarwa”
Tuni dai bankin duniya ya kebe kimanin dala miliyan dari 7 a karkashin wannan shiri na ACReSAL zuwa tsawon shekaru 7 wadda aka fara aiwatar da shi tare da hadin gwiwa da gwamnatocin jihohi 19 na arewa da gwamnatin tarayyar Najeriya.
Saurari cikakken rahoto daga Mahmud Ibrahim Kwari:
Dandalin Mu Tattauna