Da safiyar Yau ne aka ji wata kara mai kama da tashin bom a unguwar Sabon Gari da ke birnin Kano na arewacin Najeriya, wadda ta yi sanadin rasa rayukan mutane akalla biyar tare da raunata wasu da dama.
Al’amarin dai ya faru ne a layin Aba Court Road, a wani shagon dake dauke wasu sinadarai wanda don haka abin ya kara haddasa mummar karar fashewar ta iskar gas.
Wasu da abin ya faru akan idonsu sun bayyana abin da suka gani, "Sakamakon haka, muka fara kawo dauki, inda muka dauki wadanda suka samu raunuka." a cewar dayansu. Abin ya shafi wajen welda da shagon sinadarai da kuma ginin wani club dake kusa da wajen.
Daruruwan jam’ian tsaro da ‘yan sanda, sojoji da Dss da sauran hukumomin tsaro da ma masu kawo agajin gaggawa ne suka hallara a wajen.
Mataimakin Gwamnan kano, Nasiru Yusuf Gawuna, ya bukaci alu'mma da su kwantar da hankalinsu. Ya ce "Wannan al’amarin ya faru ne a wuri na yan welda; ba bom ba ne. Idan mutum ya je ya yada abin da ba haka yake ba, wace riba mutum zai samu?"
Kwamishinan yan sandan kano, Samaila Dikko, ya ce jami'an tsaro na iyakacin kokarinsu waje shawa kan al'ammarin. "Akwai sojojina sama da kasa da ma masu fararen Kaya - Kuma wani ne mai aikin welda, mai suna Vincent, a shagonsa al’amarin ya faru …"
Kawo yanzu dai an tabbatar da mutuwar mutane biyar da jikkatar wasu da dama, yayin da ake cigaba da zakulo wasu da gini ya binne su, sannan al’amarin ya faru ne daura da wata makaranta ta Winner Academy dake daura da inda abin ya faru.
Saurari rahoton Baraka Bashir: