Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasa Ta Binne Fiye Da Mutane 100


Shugaban kasar Colombia ya tabbatar da mutuwar mutane fiye da 100 a kasar ta Colombia sakamakon ruwan sama mai tsananin yawa da ya jawo kasa ta binne su a yau Asabar.

A yayin da shugaban kasa Juan Manuel ya isa Mocoa in da ya kaddamar da Matakin gaggawa shugaban yace “Yan zun nan aka bani rahoton mutane kimanin 112 ne suka mutu, kuma zamu cigaba da dubawa.”

Yayi gargadin mai yiwuwa adadin mutanen da suka rasu ya karu a yayin da ake aikin cigaba da ceton wadanda suka tsira da rayukansu.

Gwamna Sorrel Aroca na Bangaren Putamayo ya fadawa gidan radion W cewa, “Wani mummunan al’amarine da bamu taba fuskantar irinsaba” gwamnan ya kara da cewa akwai Daruruwan Iyalai da har yanzu ba’a ganosu ba haka kuma unguwanni da dama sun bace.”

Tsananin ruwan sama ya jawo Ambaliyar da ta zaizaye kasa da tabo ya binne Birnin a daren jiya Juma’a.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG