Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashe 9 Na Yankin Sahel Sun Yi Taron Sassautawa Juna Shigi Da Fici


'Yan dako a kasar jamahuriyar Nijer su na sauke lodin kayan abinci daga manyan motocin 'yan kasuwa
'Yan dako a kasar jamahuriyar Nijer su na sauke lodin kayan abinci daga manyan motocin 'yan kasuwa

A wajen taron 'yan kasuwar kasar Nijer sun koka da makotan kasashe da kuma jami'an kwastam

A jamahuriyar Nijer wakilan kasashe tara na kungiyar yaki da hamada a yankin Sahel ta C.I.L.S.S a takaice sun yi wani taron wuni daya a birnin Niamey domin duba hanyoyin shawo kan matsalolin shigi da fici da bunkasa huldar kasuwanci tsakanin kasashen tara da su ka hada da Burkina Faso, Capo-Verde, Gambia, Guinée-Bissau, Mali, Mauritania, Niger, Sénégal, da kuma Tchadi. Taron ya samu halartar jami’an tsaro da kungiyoyin fararen hula da kuma na ‘yan kasuwa. Daga Niamey babban birnin kasar jamahuriyar Nijer ga wakilin Sashen Hausa Abdoulaye Mamane Amadou da ci gaban labarin.

Taron kasashe 9 na yankin Sahel a birnin Niamey - 2:21
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:21 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG