Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen LIPTAKO Sun Kuduri Anniyar Yaki da Ta'adanci


Shugabannin kasashe ukkun dake cikin kungiyar LIPTAKO
Shugabannin kasashe ukkun dake cikin kungiyar LIPTAKO

Bayan taronsu na kwana biyu da suka yi a Yammai babban birnin Nijar,ministar harkokin raya kasa ta Nijar Hajiya Aishatu ta karanta jawabin bayan taro

Tace bayan da ayyukan ta'adanci ke kara yawaita a kasashen ukku shugabannin sun kuduri yin damarar yaki da 'yan ta'ada a kasashensu ba tare da bata wani lokaci ba..

Kasashen sun kuduri kafa rundunar hadin gwuiwa domin yakar 'yan ta'ada. Rundunar ce aka dankawa wuka da nama a yankunan kasashensu domin a kawar da 'yan ta'ada. Kungiyar tace tana kan bakanta na goyon bayan matakan da kasashen sahel suka dauka domin yaki da 'yan ta'adan.

Sun kara sanarwa cewa kungiyar na goyon bayan kungiyar dake fafatawa da 'yan ta'ada.

Taron na birnin Yammai ya bukaci skatariyar taron da ta hanzarta wurin shigo da kayan aiki ba tare da bata lokci ba saboda an dukufa da aiki gadan gadan.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:06 0:00
Shiga Kai Tsaye


.

XS
SM
MD
LG