Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Bada Umarnin Sakin Mutane 313 Da Ake Zargi Da Ta'addanci - Shelkwatar Tsaron Najeriya


 Daraktan Yada Labaran Ma'aikatar Tsaron, Manjo Janar Edward Buba
Daraktan Yada Labaran Ma'aikatar Tsaron, Manjo Janar Edward Buba

A ranar Alhamis ne Shelkwatar Tsaron Najeriya ta bayyana cewar, Babbar Kotun Tarayya dake Borno ta bada umarnin sakin akalla mutane 313 da sojoji suka kana a bisa zarginsu da aikata laifin ta'addanci.

WASHINGTON DC - A jawabinsa ga manema labarai a Abuja game da ayyukan sojojin, Daraktan Yada Labaran Ma'aikatar Tsaron, Manjo Janar Edward Buba, yace kotun ta bada umarnin sakin mutane ne saboda rashin samun gamsashiyar hujjar dake tabbatar da laifinsu bayan kammala bincike.

"A makon da muke ciki, a wani bangare na aiwatar da umarnin babbar kotun tarayya dake Maiduguri, za' a mikawa gwamnatin jihar Borno mutane 313 da ake zargi da aikata ta'addanci".

"Kotun ta bada umarnin sakin mutane ne saboda rashin samun gamsassun hujjoji bayan kammala bincike akan lamarin".

Kakakin ma'aikatar tsaron ya kara da cewar, "saboda haka, za'a mika mutanen ga gwamnatin jihar Borno domin cigaba da tuhuma", inda ya cigaba da cewar "sashen shigar da kararraki da hadin gwiwar ma'aikatar shari'a ta tarayya ne suka gurfanar da mutanen.

Ya kuma yi karin haske game da batagarin da sojoji suka kama a sassan kasar nan daban-daban.

A shiyar arewa maso gabas, dakarun aikin wanzar da zaman lafiya na "Operation Hadin Kai" sun hallaka akalla 'yan ta'adda 50 a jihohin Borno da Adamawa.

An hallaka masu tada kayar bayan da ake zargin mayakan kungiyoyin Boko Haram da ISWAP ne a kananan hukumomin Gwoza da Gamboru Ngala da Bama dake jihar Borno da kuma karamar hukumar Madagali dake jihar Adamawa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG