Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Kolin Pakistan Ta Yanke Hukuncin Hana PM Kasar Ci Gaba Da Aiki

Gungun 'yan Pakistan a wata zanga-zanga.
Gungun 'yan Pakistan a wata zanga-zanga.

Kotun kolin kasar Pakistan ta yanke hukuncin hana Friminista Yousaf Raza Gilani ci gaba da rike mukaminsa na friminista, matakin da ake ganin ka iya jefa kasar Pakistan cikin wani sabon hargitsin siyasa.

A zaman da kotun kolin Pakistan tayi talata, ta bada hujjar yanke hukuncin bisa dogaro da hukuncin farko da ta yanke game da samun Gilani da laifin rena kotu, lokacin da yaki aiki da umarnin kotun na kafa hukumar binciken da zata bincik zargin cin hanci da Rashwar da ake yiwa shugaba Asif Ali Zardari.

Cif Jojin Pakistan Iftikhar Chaudhry ya yanke hukuncin cewar tun daga ran 26 ga watan Afrilu Gilani ya kamata ya sauka daga kujerar friminista. Yanzu kuma kotun kolin ta baiwa shugaba Zaradari umarnin shirya zaben sabon friminista.

XS
SM
MD
LG