Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotunan Da Mu Ke Da Su A Najeriya Sun Wadata Wajen Shari'un Cin Hanci - Shugaban ICPC


Shugaban Hukumar ICPC, Dakta Musa Adamu Aliyu
Shugaban Hukumar ICPC, Dakta Musa Adamu Aliyu

Shugaban hukumar yaki da cin hanci ta ICPC, Dakta Musa Adamu Aliyu ya ce ba lalle sai an kafa kotuna na musamman ba don sauraron shari'un cin hanci da rashawa.

Dakta Aliyu ya fadi hakan yayin da ya ke magana a taron manema labarai a yau Litinin, 19 ga watan Fabrairun da mu ke ciki, a birnin tarayyar Najeriya, Abuja.

Hakan ya yi hannun riga da matsayar magabata a yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya.

“Ba sai an kirkiro kotuna na musamman ne za a iya gudanar da shari’un wadanda a ke tuhuma da almundahan ba, don wadanda a ke da su sun wadatar”, a cewar Dakta Aliyu.

Dakta Aliyu daga jihar Jigawa, wanda kusan shi ne mafi karancin shekaru da ya zama shugaban ICPC, ya ce don cimma nasarar shari’un ma zai rika zuwa kotu da kansa.

Ra'ayin Dakta Aliyu ya sha bamban da na masu sharhi da ma tsoffin masu ruwa da tsaki na hukumomin yaki da cin hanci da ke ganin akwai bukatar kafa kotunan yaki da cin hanci, don ta hakan ne kawai za a iya samun nasarar yaki da masu karkatar da dukiyar jama'a.

Ga matsayar tsohon kakakin hukumar EFCC, Dakta Othman Abubakar “cin hanci da rashawa laifi ne wanda sai kotun musamman ta saurara.

“Kotun musamman din ba wai cewa mala’iku ne za su zo su zauna a kotun ba, a’a, lauyoyin dai da mutane masu basira su suke hadawa a yi irin wadannan (tribunal) amma a yanda a ke tafiya a kotunan Najeriya abun bacin rai, ba za a je ko ina ba.”

In za a tuna, tsohuwar Shugabar EFCC, Hajiya Farida Waziri ta ce ba ma batun kotuna ba ne kawai, akwai bukatar gwajin kwakwalwar barayin biro.

Sabon Shugaban na ICPC wanda ya yi alwashin yin aiki tare da sauran hukumomin yakin, ya ba da tabbacin samar da sauyin da jama’a za su shaida hakikanin yakin.

Najeriya na da hukumomin yaki da cin hanci da sun kusan yatsun hannu kamar EFCC, ICPC, Kotun Da’ar Ma’aikata, Kwamitocin Shari’a amma sai a wayi gari a na zargin babban jami’in gwamnati da wawure biliyoyi ko ma tiriliyoyin Naira.

A saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya:

Kotunan Da Mu Ke Da Su A Najeriya Sun Wadata Wajen Shari'un Cin Hanci - Shugaban ICPC
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:50 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG