Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Hadin Kan Kasashen Afrika Ta Ce Dole Ne a Ja Wa Tarzomar Burundi Burki


Shugaba Pierre Nkurunziza.
Shugaba Pierre Nkurunziza.

Kungiyar Hadin Kan Kasashen Afrika ta ce dole a daina tashin hankalin da ke addabar kasar Burundi, ta na mai cewa ba za ta kyale kasar ta abka cikin rigimar da za ta kai ga kashe-kashen kiyashi ko na gilla ba.

Kwamitin Zaman Lafiya da Tsaro na Kungiyar AU na da damauwa ne akan gudun kada a bar rikicin siyasar da ke faruwa yanzu a Burundi ya sake jefa kasar a cikin tarzoma mai kama da wacce ta faru a shekarar 1994 a kasar Rwanda, wacce ta janyo mutuwar dubban mutane da yawa.

Kwamishinan Samarda Zaman lafiya da Tsaro, Smali Cherugi ya fada a wajen taron AU da ake yau a birnin Addis Ababa na kasar Ethiopia cewa, matsayin AU guda daya ne tak: dole a ja wa wannan tarzomar ta Burundi burki.

A yau Alhamis ne ake sa ran cewa Cibiyar Kare Hakkin Bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya za ta jefa kuri’a akan shawarar da Amurka ta gabatar ta ko a tura wata tawaggar masana zuwa can Burundi don suje su ga abinda ke faruwa, kana su bada shawarwarin matakan da za’a dauka kan tashe-tashen hankullan.

Labarai masu alaka

XS
SM
MD
LG