Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Kungiyar AU Na Nemo Hanyar Warware Matsalolin Dake Addabar Nahiyar Afirka


Taron Kungiyar AU a Birnin Addis Ababa
Taron Kungiyar AU a Birnin Addis Ababa

Shugabannin kasashen Afirka sun bude wani taro na kwanaki biyu a ranar Asabar, yayin da nahiyar ke kokawa da juyin mulki da rigingimu da rikicin siyasa da kuma zaman dar dar a yankin.

Gabanin taron da za a yi a Addis Ababa babban birnin kasar Habasha, shugaban hukumar Tarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat, ya yi tsokaci kan tashe-tashen hankula da ke addabar kasashe da dama, na Afirka da sauran sassan duniya.

Sudan na cikin “rikici,” in ji Faki, yayin da yake bayyana barazanar ‘yan ta’adda a Somaliya, da “rikicin marar karewa” a gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, da “hadarin ta'addanci” a yankin Sahel, da kuma rashin zaman lafiya a Libya.

“Sake dawo da juyin mulkin soji da tashin hankali kafin zabe da bayan zabe, da rikicin jin kai da ke da nasaba da yaki da/ko kuma illar sauyin yanayi, duk wani abu ne mai matukar damuwa a gare mu,” kamar yadda ya shaida wa ministocin harkokin wajen Afirka a ranar Laraba.

An bude karamin taron kolin da nufin lalubo hanyoyin sake kaddamar da shirin samar da zaman lafiya ga DRC -- ciki har da shugaban Congo da abokin hamayyarsa na Ruwanda -- wanda aka bude ranar Juma'a a gefen manyan tarukan kungiyar AU, kuma zai ci gaba a ranar Asabar.

Sai dai an dade ana sukar kungiyar mai mambobi 55 da cewa ba ta da wani tasiri, kuma ba ta dauki kwararan matakai ba wajen fuskantar tashe-tashen hankula da kwace madafun iko.

Nina Wilen, darektar shirin Afirka a cibiyar nazarin huldar kasa da kasa ta Egmont Royal da ke Brussels, ta ce “Ina shakkun cewa za a yanke hukunci mai karfi.”

Ya zuwa yanzu dai kungiyar ta kasashen Afirka ba ta da wani tasiri sosai kan kasashen da suka fuskanci juyin mulkin baya-bayan nan, in ji ta, ta kuma kara da cewa kasashe mambobin kungiyar ba sa son kafa abubuwan da za su ci karo da muradunsu.

Daga cikin wadanda suka halarta daga wajen yankin har da shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva. Sai dai babban sakataren MDD Antonio Guterres bai halarci taron ba, yayin da mai magana da yawunsa Stephanie Tremblay ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP, cewa yana da matsalar jirgin sama kuma bai samu damar tashi zuwa Addis Ababa ba.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG