Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin Sa Kai Sun Dankawa Iyalai 75 Amanar Marayu 150 A Adamawa


Marayu da Magidantan da aka amanarsu
Marayu da Magidantan da aka amanarsu

Kungiyoyin JANNA Founation da Best Agenda tare da hadin gwuiwra Gidauniyar tallafawa wadanda rikicin Boko Haram ya shafa da Janar T.Y Danjuma ke jagoranta sun tanadi tallafi na naira dubu goma sha hudu kowane wata ga marayu dari da hamsin ‘yan kasa da shekara goma sha biyu don taimakawa iyalai saba’in da biyar da suka amshi amanar kulawa da su a Mayo-Konkol na karamar hukumar Maiha dake jihar Adamawa.

Ana tsara shirin don tallafawa ta hanyar ilimantarwa, kula da lafiya da tarbiyartarda marayun na tsawon shekara daya wanda ya soma aiki daga watan Nuwambar shekarar 2016 inji daraktan kungiyar JANNA Foundation Dr. Abdullahi Balel.

Domin gujewakada marayun su fada hannun iyaye maras adalci kungiyoyin sun yi anfani da sarakunan gargajiya, malaman addini da jami’an sashin kula da rayuwar jama’a na karamar hukumar wajen tantance iyalan da aka dankawa amanar kulawa da marayun.

Shima da yake jawabi a wajen kaddamar da shirin darakta janar na Best Agenda Alhaji Ahmed Lawal ya tunatar da iyayen cewa amanar kula da marayun da suka karba Allah zai yi anfani da shi a matsayin minzanin gwajin kaifin imani da suke da shi, saboda haka ya shawarcesu su kaucewa nuna bambanci sakanin ‘ya’yan cikinsu da na riko da aka ba su.

Wasu daga cikin iyayen da wakilin Muryar Amurka ya yi hira da su Malam Mohammed Abba da Malama Jummai Mika’ilu sun bayyana mataki da kungiyoyin suka dauka da alamu ne na tausayawa tare da alkawarin anfani da bitar da suka karba wajen kula da marayun.

Ga rahoton Sanusi Adamu da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00

XS
SM
MD
LG