Mutane kimanin biyar sun mutu zuwa yanzu a jihar Kano bayan da kimanin mutane 189 su ka kamu da cutar kwalara ko amai da gudawa a Kanana Hukumomi 20 a jahar, inda daga cikinsu mutane 184 su ka warke. Cutar ta fara kama mutane ne tun daga watan Afirilu.
Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Aminu Tsanyawa ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai jiya Talata. Kwamishinan ya ce dama akan samu barkewar cutar ta kwalara a daidai wannan lokacin a kusan kowace shekara.
Ya ce akwai bukatar a tuna cewa a lokacin damina, saboda rashin tsaftar muhalli da kuma na jama’a – ciki har da zubar da shara barkatai, yin bayan gida a fili da rashin sarrafa abinci ta hanya mai tsafta, wadanda dukansu ke yada cutar tsakanin jama’a.
Dakta Tsanyawa ya ce Hukumar Yaki Da Cututtka ta Kasa (NCDC), ta samu mutane 2,339 dauke da cutar ta kwalara a jihohi sama da 30 tun daga watan Janairu zuwa watan Yunin 2022.
Ya ce tuni Ma’aikatar Lafiya ta jihar ta Kano ta dau matakin shawo kan cutar.
Saurari jawabin Kwamishinan, wanda Baraka Bashir ta turo ma na: