Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mafi Yawan Kasashen Duniya Sun Amince Da Tsagaita Wuta a Gaza


Zauren Majalisar Dinkin Duniya
Zauren Majalisar Dinkin Duniya

Babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri'a da gagarumin rinjaye a ranar Talata, inda ya bukaci a gaggauta tsagaita wuta tsakanin Hamas da Isra'ila tare da sakin mutanen da kungiyar Hamas da kawayenta suka yi garkuwa da su ba tare da wani sharadi ba.

A kuri'ar da kada a zauren Majalisar Dinkin Duniya, kasashe 153 sun amince amma kasashe 10 sun yi adawa da shirin, majalisar ta amince da wani kuduri na neman "tsagaita wuta domin ayukan jin kai cikin gaggawa," da kuma sakin dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su ba tare da wani sharadi ba, kazalika da ba da tabbacin samun damar shiga Gaza.

"Yau rana ce mai cike da tarihi dangane da gagarumin sako da aka aike daga babban zauren Majalisar," in ji wani mai farin ciki Riyad Mansour, wakilin Falasdinawa, a wata zantawa da manema labarai. “Kuma hakki ne na hadin gwiwa mu ci gaba da tafiya a kan wannan tafarki har sai mun ga an kawo karshen wannan ta’addancin da ake yi wa jama’armu, don ganin an daina yaki da mutanenmu. Wajibi ne mu ceci rayuka.”

Sama da kasashe 100 ne suka goyi bayan wannan daftari, wanda wasu gungun kasashen larabawa da na musulmi suka tsara, kuma ya kasance daidai da wanda Amurka ta ki amincewa da shi a ranar Juma’a a kwamitin tsaro mai karfin kasashe 15.

Amurka ta yi kokarin shigar da gyara a cikin daftarin majalisar wanda ya yi Allah wadai da harin ta'addancin Hamas na ranar 7 ga Oktoba da kuma yin garkuwa da mutane. An kada kuri'a. Haka kuma wasu gyare-gyaren da Ostiriya ta gabatar da ke son hadawa da "Hamas da sauran kungiyoyi" kafin kalmar "masu garkuwa".

Amurka da Ostiriya na daga cikin kasashe 10 da suka kada kuri'ar kin amincewa da daftarin kudurin. Sai kuma sauran kasahen da suka hada da Isra'ila da Czechia da Guatemala da Laberiya da Micronesia da Nauru, Papua New Guinea da kuma Paraguay ne suke cikin rukunin.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG