Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawan Amurka Ta Amince da Kakabawa Rasha Takunkumi


Shugaban masu rinjaye Mitch McConnell a tsakiya da wasu sanatoci
Shugaban masu rinjaye Mitch McConnell a tsakiya da wasu sanatoci

Jiya Talata aka gabatar da dokar data samu goyon bayan dukkan jam’iyun siyasar Amirka, gaban Majalisar dattijan, da zata bukaci a kara azawa kasar Rasha takunkumi bisa zargin cewa ta yi shishigi a zaben shugaban kasar da aka yi a watan Nuwamba.

Sanata Ben Cardin dan jam’iyar Democrat wanda ya gabatar da dokar yace, a lokacinda aka kai hari Pearl Habour da kuma lokacin da aka kawo hare haren ta’adancin watan Satumban shekara ta dubu biyu da daya, sun dauki matakin tinkarar wadanda suka kawo harin da kuma daukan matakan hana aukuwar kawo wasu hare hare akan Amirka. A saboda haka yace akwai bukatar su dauki matakin bayanawa balo balo cewa duk wanda yayi irin shishigin da Rasha ta yi, ba za’a kyale ba.

An gabatar da wannan mataki ne kwanaki hudu bayan da hukumar leken asirin Amirka ta gabatar da rahoton dake zargin Rasha da laifin yin katsalanda a zaben shugaban kasar da aka yi.

XS
SM
MD
LG