Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Wakilan Najeriya Ta Gayyaci Tsohon Shugaban Kwamitin Kasasfin Kudi


 Abdulmummuni Jibrin, tsohon shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar wakilai
Abdulmummuni Jibrin, tsohon shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar wakilai

Kodayake an ce majalisar wakilan Najeriya ta dakatar da Abdulmummuni Jibrin tsohon shugaban kawamitin kasafin kudi saboda ya zargi majalisar da yiwa kasafin kudin kasa coge, majalisar ta zargeshi da laifuka biyu, wato rashin zuwa aiki da kuma wai yana aiki da asusun banki na kasashen waje.

Majalisar ta gayyaci Abdulmummuni Jibrin ya zo majalisar ya kare kansa bisa ga laifuka biyun da majalisar ke zargin ya aikata.

Daya cikin 'yan majalisar Timothy Ngolu ya nuna suna da hujjar gayyatar shi Jibrin saboda wai su masu jin kukan mutane ne. Wajibi ne su kirashi su bayyana masa abubuwan da suke zarginshi da yi da kuma korafe korafen da suka samu a kansa. Ngolu yace dole ne su ji daga bakinsa.

Akan cewa Abdulmummuni Jibrin ya daina zuwa majalisar ne saboda majalisar ce ta koreshi sai Timothy Ngolu ya musanta batun. Yace akwai doka akan zuwa majalisa kuma wanda yaki kotu na iya yin waje dashi daga majalisar

Shi ma Yuguda Hassan Kila mai wakiltar mazabar Gwaram jihar Jigawa yace matakin da majalisar ta dauka na son jin ta bakin Abdulmummuni Jibrin shi ne adalci. Suna bukatan su yi masa tambayoyi idan shi kuma yana da tambayoyi sai yayi masu.

Shi dai Abdulmummuni yayi alkawarin bayyana a gaban majalisar idan ya samu wasika a hukumance.

Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:30 0:00

XS
SM
MD
LG