Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisun Najeriya na Jan Kafa Kan Gyara Kundun Tsari


'Yan Najeriya suna kokarin gina muhalli
'Yan Najeriya suna kokarin gina muhalli

Kungiyar kananan hukumomi a Najeriya ko NULGE a takaice, ta dade tana fafitikar a gyara kundun tsarin mulkin kasar su ci gashin kansu su kuma samu naso kason kudi daga gwamnatin tarayya.

Kawo yanzu tamkar kananan hukumomi basu da 'yanci. Gwamnonin jihohinsu sai sun ga dama suke shirya zabuka wadanda idan ma an yi nadi gwamnoni ke yi. Ban da haka hukumomin basu samun naso kason kudi kai tsaye daga gwamnatin tarayya. Kasonsu na bin hannun gwamnoninsu ne wadanda sai sun ga dama suke basu.

Dalili ke nan da ma wasu dalilai da kananan hukumomi suke neman a yiwa kundun tsarin mulkin kasar kwaskwarima. Gyaran zai basu 'yanci zasu kuma iya yin zabe lokacin da dokar ta tanada. Ban da haka gwamnoni ba zasu iya cigaba da rushesu ba

Shugaban ma'akatan kananan hukumomi a Najeriya ko NULGE, a takaice, Alhaji Ibrahim Kalil ya ce jan kafar da majalisun kasar ke yi kan gyara kundun tsarin mulkin kasar abun takaici ne. Ya nuna takaicinsa ne a taron kungiyar da suka yi a jihar Oyo domin zaban shugabannin kungiyar ta jihar. Ya ce gaskiya akwai takaici shi ya sa mutanen Najeriya ke shakkun mulkin kasar. Abun takaicin shi ne tun da majalisar wakilai ta yadda amma ta dattawa ki zaman samun daidaituwa tsakaninsu kamar yadda doka ta tanda ya cutura.

Kan batun yin nazari, Alhaji Kalil ya ce babu wani zarari da ya saura a yi domin an yi a duk fadin kasar. An tattara jawabai har ma da kasidu kan cancantar yin gyaran domin tabbatar da cikakkiyar dimokradiya. An kuma kashe makudan kudade domin kowa ya fadi albarkacin bakinsa. Abun da ya saura kawai majalisun su zauna su bi abun da mutanen kasar ke so su kuma aiwatar.

Kamata ya yi majalisun su fito su fadawa 'yan Najeriya dalilin da ya sa suka kasa aiwatar da gyaran. Dama ana zargin wata kila gwamnoninsu suka hanasu yin abun da ya kamata. Idan ba haka ba idan kuma ba rufa-rufa ko boye gaskiya ko son yin rashin da'a suke son su nuna ma duniya ba to su fito su yi abun da jama'a suke so. Kila suna son cin amanar mutanen Najeriya ne shi ya sa suna jan kafa a KAN al'amarin.

Ga Hassan Umar Tambuwal da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:07 0:00
Shiga Kai Tsaye

.
XS
SM
MD
LG